Kamfanin gine gine na kasar wato CCECC, a jiya Alhamis, ya mika wasu rukunin azuzuwa 6 da ya yi musu kwaskwarima wanda ya lashe kudi dala dubu 80 a wata karamar hukuma da ke Legas a shiyyar kudu maso yammacin Najeriya.
Kamfanin ya gudanar da aikin gyaran ne a karamar makarantar sakandaren Abule-Ado, a matsayin gudumawar kamfanin.
Aikin ya kunshi gyara rukunin azuzuwa 6, sannan ya samar da kujerun zama 4 da tebura 2 da jakar makaranta 300 da littattafai da sauran kayayyaki ga dalibai.
Gwamnan jiar Legas Akinwumi Ambode, wanda ya samu wakilcin babban sakatare a ma'aikatar ilmi na jihar Olabisi Ariyo, ya yaba wa kamfanin na CCECC bisa wannan aikin, sannan ya yi alkawarin za su ci gaba da hada gwiwa da kamfanoni masu zaman kansu, sannan za'a samar da yanayi mai kyau ga kamfanonin domin zuba jari don samun ci gaba.
Karamin jakadan ofishin kasar Sin dake Legas Liu Kan, wanda ya mika aikin ga gwamnatin ta Legas, ya bayyana cewar, makasudin wannan aikin shi ne, domin karfafa dankon zumunta tsakanin kasar Sin da Najeriya da kuma tallafa wa ci gaban ilmin a Najeriyar.
Wakiliyar kungiyar iyayen yara da malaman makaranta Mrs Nimota Mohammed Sanni, ta bayyana cewar, a baya, yara dalibai na fuskantar wahalhalu a lokutan damina da zarar an fara ruwan sama, amma a yanzu an mayar da makarantar irin na zamani, a don haka ta gode wa kamfain na kasar Sin bisa wannan aiki.(Ahmad Fagam)