in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muna nan kasar Sin (1)
2015-12-02 18:58:22 cri

Tun bayan da aka kaddamar da taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka(FOCAC) a shekarar 2000, huldar kasuwanci dake tsakanin bangarorin 2 na dinga samun ci gaba.
A birnin Guangzhou dake kudancin kasar Sin,wanda ya kasance wata cibiyar kasuwanci ta kasar Sin, akwai wasu 'yan kasuwa Hausawa dake zama a can. Suna kokarin saye-sayen kayayyakin da suke bukata a manyan kasuwannin birnin, suna kuma tura su zuwa kasar su ta Najeriya. Hotunan da muka dauka sun nuna yadda suke gudanar da ayyukansu a birnin Guangzhou.

Alhaji Mutapha Hamza ke nan yana neman kayayyakin da yake bukata a wata kasuwar kayan lantarki. Mustapha ya yi kusan shekaru 7 yana zama a Guangzhou. A baya ya taba sayar da agogo, sa'an nan yanzu yana aikin dillancin kayayyaki.

Alhaji Mustapha Hamza yana nuna masu shago sunayen abubuwan da yake nema. Abubuwan ne da wani dan kasuwan Najeriya ya bukaci Mustapha da ya sayo masa.

Alhaji Mutapha Hamza yana shirin zuwa bikin bajekolin kayayyaki na Canton Fair.

Shaguna a wajen Canton Fair, babban bikin bajekolin kayayyaki da a kan gudanar da shi karo 2 a ko wace shekara, wanda ya kan janyo hankalin 'yan kasuwan kasashen duniya daban daban.

1 2 3 4 5 6
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China