in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta ajiye kara ga Afrika ta Kudu game da hare haren kyamar baki
2015-04-17 12:23:08 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya bayyana a ranar Alhamis cewa, kasar Sin ta ajiye kara ga kasar Afrika ta Kudu game da batun hare haren kyamar baki 'yan kasar Sin.

Shaguna da dama ne dake hannun 'yan kasar Sin aka fashe a yayin tashe tashen hankali na baya bayan nan bisa dalilin zargin da 'yan kasar Afrika ta Kudu suke yi wa bakin da shigowa cikin kasar ba bisa doka ba, suna gudanar da kasuwanci ba bisa doka ba, da kuma aikata laifuffukan kisa.

Ofishin jakadanci da kananan jakadun kasar Sin dake Afrika ta Kudu, sun yi kashedin hadura daban daban da ke tattare da wannan matsala, domin yin kira ga kamfanonin kasar da Sinawan dake wannan kasa da su kara karfafa matakan tsaronsu.

A cewar jami'in, ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, tare da ofishin jakadanci da kananan jakadun kasar Sin da ke Afrika ta Kudu za su ci gaba da kara mai da hankali, musammun ma kan halin da ake ciki, da kuma kiyaye tsaro da 'yancin 'yan kasar Sin da ke wannan kasa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China