Kwamitin tsaro na MDD ya yi allah wadai da kisan kiyashin jama'a farar hula da ake yi a jamhuriyar damokradiyyar Congo DRC.
Kwamitin ya yi kira a kan gwamnatin ta Congo da ofishin wanzar da zaman lafiya na MDD da su dauki mataki na rage barazanar da ake yiwa farar hula.
Wata sanarwar kwamitin tsaron MDD ya ce, hare-haren da ake kaiwa sun haddasa mutuwar mutane farar hula fiye da 200, tun daga tsakiyar watan Oktoba a gabashin kasar.
A cikin sanarwar, wakilin kwamitin tsaron sun mika ta'aziyyarsu ga iyalan wadanda suka rasu, tare da jaddada bukatar da ke akwai.
Kwamitin tsaron mai mambob 15 ya kara nanata bukatar dake akwai na aiki da kuduri na kwamitin tsaron na MDD mai lambar 2147 na wannan shekarar domin tabbatar da cewar, an dauki matakai na kare farar hula da 'yan tsagera masu dauke da bindiga, wadanda ke ci gaba da kasancewa a gabashin kasar. (Suwaiba)