in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Asusun gaggawa ga Afrika na kan gaba a jadawalin taron Valletta kan 'yan gudun hijira
2015-11-11 09:52:14 cri

Shirin kafa wani asusun gaggawa ga Afrika wanda zai fara da kudi euro biliyan 1.8 na kan gaba a jadawalin taron kan 'yan gudun hijira da za'a yi a Valletta, babban birnin jamhuriyar Malta, a bayanin da shugaban majalissar kungiyar tarayyar Turai Donald Tusk ya yi a jiya Talata cewa asusun zai taimaka wa mutanen Afrika samun makoma mai kyau.

A lokacin da yake bayanin a gaban mahalarta zama na musamman da aka yi a majalissar a kasar Malta, Tusk ya ce, tattalin arziki, daidaito da tsaro, har ma da gudanarwa da doka su ne manyan kalubaloli uku dake fuskantar nahiyar ta Afrika.

Ya ce, taron na Valletta wanda zai hallaro shugabannin wasu kasashen Turai da Afrika zai zama mai karko da daukan mataki. Afrika da Turai, in ji shi, ba wai suna son kirkiro sabon tsarin siyasa ba ne. Ana da shi tun tuni, kuma a baya bayan nan aka kara nanatawa a wajen taron kungiyar tarayyar Turai da Afrika a Brussels.

Maimakon haka, in ji shugaban majalissar kungiyar tarayyar Turai, ana son fidda wata mafita ne mai karko.

Ana sa ran shugaban kungiyar tarayyar Turai Jean-Claude Juncker a ranar Alhamis din makon nan zai rattaba hannu a kan asusun gaggawan na Afrika, daya daga cikin matakan da aka tsara don maida martani ga halin 'yan gudun hijira da ake fuskanta a yanzu.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China