Shugaban majalisar dattawan jamhuriyar demokuradiyar Congo DRC Leon Kengo Wa Dondo ya bude taron tattalin arzikin Afrika (AEC) karo na goma a ranar Litinin a birnin Kinshasa, wanda kuma a wannan shekara aka dora muhimmanci kan yaki da talauci da bambance bambance a nahiyar Afrika.
Taken taron na wannan karo, shi ne "Yaki da talauci da bambance bambance a cikin shirin bunkasuwa na bayan shekarar 2015".
Taron dake gudana tun daga ranar 2 zuwa 4 ga watan Nuwamba, ya samu halartar masu fada a ji, kwararru a fannin ci gaba da kuma masana, inda suke tattauna hanyoyin da za a bi domin kawar da talauci, da kuma yadda za'a magance bambance bambance a nahiyar Afrika a cikin tsarin sabbin maradun duniya na yaki da talauci. (Maman Ada)