in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Zimbabwe ya yaba wa Sin game da tallafinta na tattalin arziki
2015-08-26 10:22:23 cri

Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya nuna yabo a ranar Talata ga kasar Sin kan tallafinta a kokarin sake farfado da tattalin arzikin kasarsa.

A cikin wani jawabi zuwa ga 'yan kasarsa, shugaba Mugabe ya yi imani da muhimmin tallafin Sin a bangarorin da suka hada da makamashi, kiwon lafiya, sadarwa, da kuma noma.

Haka kuma ya kawo batun tallafin kiwon lafiya da kasar ta Sin ta bayar bisa wani rancen kudi na dalar Amurka miliyan 90, tare da kafa wata cibiyar sadarwa mafi inganci ta internet (HPC) a jami'ar Zimbabwe a cikin watan Febrairun da ya gabata.

Cibiyar kwamfuta mafi girma da inganci ta uku a Afrika, HPC, za a iya yin amfani da ita a harkokin tattalin arziki da jama'a, hasashen lokaci, yanayi, da ma sauran abubuwa da nufin taimaka wa masu fada a ji a kasar, in ji Mugabe.

Bisa tsarin rance a fannin kiwon lafiya, Zimbabwe ta samu kayayyaki iri daban daban domin tafiyar wasu gine ginen kiwon lafiya na musammun, da motocin likita na musammun da sauransu.

Domin zamanintar da ababen more rayuwa, mista Mugabe ya bayyana cewa, Zimbabwe tana neman kudade a cikin gida da kuma waje domin wadannan muhimman tsare tsare.

Gwamnatin Zimbabwe ta rattaba hannu kan wasu muhimman ayyuka tare da kasar Sin da suka hada da makamashi, hanyoyi, layukan dogo, sadarwa, ruwa, noma, ma'adinai da kuma yawon bude ido, in ji shugaba Mugabe. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China