Kwamitin tsaro na MDD a ranar Lahadin nan 4 ga wata ya yi kakkausar suka a kan mummunan harin da aka kai na bam a Mogadishu, babban birnin kasar Somaliya, yana mai kiran shi da na ta'addanci, sannan ya jaddada goyon bayansa ga bukatar samar da zaman lafiya da tattaunawar sulhu a kasar.
Mambobin kwamitin sun yi suka a kan harin da kungiyar Al-Shabaab ta dauki alhakin aiwatarwa, abin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama, wassu kuma suka samu raunuka, kamar yadda wata sanarwa da kwamitin mai wakilai 15 ya fitar.
A bisa ga bayanai da aka fito, wani bam ne da aka ajiye a gefen titi mai cike da jama'a ya tarwatse a Mogadishu a ranar Asabar, wanda nan take ya hallaka mutane 6, wassu guda 7 kuma suka ji rauni.
Kungiyar masu tsattsauran ra'ayin addinin islama Al-Shabaab ta sanar da kai wannan harin domin ta samu motar wani tsohon jami'in gwamnati da ke wucewa a daidai wannan lokaci wanda shi ma ya hallaka a cikin harin. (Fatimah)