in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD ya yi allawadai da kisan 'dan majalisa a Somaliya
2014-07-04 10:15:26 cri

Kwamitin tsaro na MDD ya yi allawadai da babbar murya a ranar Alhamis da kisan gilla kan wani mamban majalisar tarayyar Somaliya, Ahmed Mohamud Hayd, da mayakan kungiyar Al-Shabaab suka dauki alhakinsa.

Haka kuma wannan hari ya yi sanadiyyar mutuwar wani jami'in dake tsaron lafiyar 'dan majalisar, da jikkata wasu mutane da dama.

A cikin wata sanarwa, mambobin kwamitin tsaro sun gabatar da ta'aziyarsu ga iyalan da wannan al'amari ya shafa, al'ummar kasar da kuma gwamnatin Somaliya, tare da fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata.

Mambobin kwamitin tsaro sun bayyana a cikin sanarwar, inda suka nuna damuwa da bacin rai ga yadda Al-Shabaab ta kai wannan hari ba ji ba gani ga wani mamban majalisar Somaliya, wata hukumar dake wakiltar fatan alherin al'ummar Somaliya, da kuma makoma mai haske bisa tsarin demokaradiya, zaman lafiya da cigaba.

Manzon musamman na sakatare janar na MDD game da kasar Somaliya, Nicholas Kay, shi ma ya yi allawadai a ranar Alhamis da wannan kisa na 'dan majalisa a Mogadishu, birnin dake fama da hare-haren mayakan Al-Shabaab tun farkon watan Azumi. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China