in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A Najeriya 'yan adawa sun soki manufar rage darajar kudi
2014-11-27 10:48:00 cri

Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya APC, ta soki gwamnatin kasar mai ci, game da manufar rage darajar kudin kasar, manufar da ta bayyana da wani mataki da ka iya lahanta tattalin arzikin kasar.

A ranar Laraba ne dai babban bankin kasar ya sanar da rage darajar kudin kasar, sakamakon wasu dalilai da suka hada da faduwar darajar danyan mai a kasuwannin duniya. Bankin na CBN ya kuma ayyana sabon farashin canjin dalar Amurka, wanda a yanzu ko wace dala za ta kasance kan naira 168, sabanin naira 155 da a baya ake canza dalar.

Da yake tsokaci game da daukar wannan mataki, kakakin jam'iyyar adawar ta APC Lai Mohammed, ya shaidawa manema labaru cewa, wannan mataki zai shafi ci gaban tattalin arziki, tare da sake jefa 'yan Najeriyar cikin mawuyacin hali.

Ya ce, a baya, jam'iyyar sa ta sha jan hankalin mahukuntan kasar, game daukar matakan da suka dace domin kaucewa fadawa makamancin wannan hali.

Najeriya dai ta fada halin tsaka mai wuya ne tun bayan da OPEC ta mai da farashin danyan mai zuwa dala 77.27, wanda ya yi kasa da mizanin kasafin kudin kasar na bara, da aka dora bisa farashin dala 78 kan kowace gangar danyan man. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China