Mahukuntan kasar Rwanda sun aike da jami'an 'yan sanda 170 da suka hada da mata 40 zuwa Sudan ta Kudu, domin tallafawa ayyukan rundunar MDD mai aikin wanzar da zaman lafiya a kasar. Tuni dai jami'an tsaron suka isa birnin Malakal mai nisan kilomita 165 daga Juba.
A cewar kakakin rundunar 'yan sandan kasar ta Rwanda Celestin Twahirwa, wannan ne rukuni na farko na tawagar 'yan sandan kasar da aka aike zuwa Sudan ta Kudu. Twahirwa ya ce, jami'an za su baiwa ofisoshin tawagar UNMISS dake sassan Sudan ta Kudu kariya, a hannu guda kuma MDD za ta dauki nauyin ayyukan jami'an, ta fuskar tsare-tsaren aiki, da kuma kudaden gudanarwa.
Bisa jimilla, kasar Rwanda ta aike da jami'anta 2,623 zuwa kasashen gabashin Afirka daban daban, inda suke gudanar da ayyukan wanzar da zaman lafiya karkashin inuwar MDD, da kungiyar tarayyara Afirka ta AU, kamar dai yadda shafin yanar gizo, na rundunar 'yan sandan kasar ya bayyana.(Saminu)