A ranar Talatar nan, bangarori a Sudan ta Kudu da suka hada da na gwamnati da 'yan tawaye, har ma da bangaren tsoffin fursunonin kasar sun rattaba hannu kan yarjejeniyar wanzar da zaman lafiya a kasar.
Ana sa ran wannan ce yarjejeniya ta karshe da za ta kawo karshen tashin hankali a kasar, da kuma tsagaita bude wuta, bayan gudanar da tattaunawa ta tsawon kwanaki 14 a birnin Addis Ababa na kasar Habasha.
IGAD ce ke shiga tsakani domin ganin an samu nasarar kawo karshen tashin hankali a Sudan ta Kudun tun bayan barkewar rikicin a tsakiyar watan Disambar shekarar 2013.
Tuni dai bangarorin gwamnatin kasar da na sojojin fafutukar 'yancin Sudan wato SPLM/SPLA da na tsoffin fursunonin kasar suka sanya hannu kan yarjejejiniyar.
Manzon musamman na IGAD, kuma tsohon shugaban kasar Bostwana Festus Mogae, ya kasance a matsayin shaida a yayin rattaba hannu kan yarjejeniyar.
Ministan yada labaran Sudan ta Kudun Michael Makuei, ya bayyana cewar, wannan muhimmiyar rana ce ga al'ummar Sudan ta Kudun, kasancewar ranar da aka fara aiwatar da jarjejeniyar da ake sa ran za ta kawo karshen zaman tankiya a kasar.
Ministan ya ce, bangaren gwamnati a shirye yake ya tabbatar da ganin an mutunta wannan yarjejeniya yadda ya kamata.
Shi ma Janar Taban Deng, shugaban SPLM zai isa babban birnin kasar Juba kan wannan batu.
Wakilin tsoffin fursunonin Sudan ta Kudun John Luk Jok, ya bayyana ranar da cewa lokaci ne mai dunbun tarihi kan shirin samar da zaman lafiyar kasar.(Ahmad Fagam)