Bangarori biyu dake arangama da juna a kasar Sudan ta Kudu a ranar Litinin din nan suka zargi junansu da karya yarjejeniyar da aka shimfida ta tsagaita bude wuta wadda suka rattaba wa hannu a watan Agusta, kamar yadda gidan radiyon Tamazuj ya bayyana.
Tun safiyar ranar Lahadi, sojojin gwamnatin ke luguden wuta a yankunan dake karkashin ikon bangaren 'yan adawa dake kudancin Malakal, kamar yadda gidan radiyon ta ruwaito kakakin babban kungiyar 'yan tawayen kasar William Gatjiath.
Sai dai kuma kakakin gwamnatin kasar Philip Aguer ya musanta wannan zargin, yana mai cewa, sojojin kasar ba su yi wani yunkuri a yankin Upper Nile ba, kuma ba su tunkari wani yankin da yake karkashin ikon 'yan tawaye ba.
Har ila yau ya zargi bangaren adawa karkashin jagorancin tsohon shugaban kasar Riek Machar da kai hari a kan yankunan dake karkashin ikon gwamnati kamar su Wadakona.
Bangarorin biyu dake arangama da juna a kwanan nan suka tabbatar da cewa, za su amince da tsagaita bude wuta kamar yadda yarjejeniyar zaman lafiyar da bangarorin biyu suka cimma karkashin jagorancin kungiyar IGAD a karshen Agustan da ya gabata.
Sai dai kuma bangarorin biyu suna ci gaba da zargin juna da saba ka'idar tsagaita bude wuta. (Fatimah)