in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Magajin garin Rio ya tabbatar da samun ingantaccen tsaro a lokacin gasar wasannin Olympic
2015-11-25 15:37:02 cri
Magajin garin birnin Rio de Janeiro Eduardo Paes, ya ce hukumomin kasar Brazil zasu hada kai da hukumomin leken asiri na kasa da kasa domin tabbatar da tasron birnin, a yayin gudanar da gasar wasannin motsa jiki ta Olympic a shekara mai zuwa.

An shiga zulumi na fargabar tsaro ne, tun bayan harin ta'addanci na ranar 13 ga watan Nuwambar wannan shekara a birnin Paris wanda yayi sanadiyyar rayukan muatane 130.

Mista Paes ya tabbatarwa manema labarai cewar, an yi kyakkayawan tanadi dangane da tsaro, kuma za'a maida hankali wajen ci gaba da tabbatar da tsaron.

Ya ce dole a shigo da hukumomin leken asiri na duniya ba tare da wata kunbiya kunbiya ba.

Shi dai mista Paes, ya yi wannan karin haske ne bayan kammala wata ganawa da tawagar wakilan kwamitin shirya gasar wassannin Olympic ta duniya wadan da suka ziyarci birnin na Rio, domin duba ci gaban da aka samu a shirye shiryen karbar bakuncin gasar, wanda ake saran gudanarwa a daga ranar 5 zuwa 21 ga watan Augusta na shekarar badi.

Ya ce a halin ake ciki, babu koda mutum guda daga cikin tawagar kwamitin na IOC da ya nuna fargaba dangane da yanayin tsaro.

Daga cikin batutuwan da aka tattauna a taron, akwai batun rage kudaden kasafin kudi na shirya wasannin wanda kwamitin yayi alkawar tun da farko, domin kaucewa fitar da kudaden da suka wuce kima.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China