in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Laberiya ta tabbatar da mutuwar wani matashin da ya kamu da Ebola
2015-11-25 10:20:10 cri

Ma'aikatar kiwon lafiya kasar Laberiya ta tabbatar a ranar Talata cewa, wani matashi mai shekaru goma sha biyar da aifuwa ya mutu sakamakon cutar Ebola, kuma wannan ne karo na farko da wannan cuta ta yi sanadiyyar mutuwar wani mutum tun bayan da wannan kasa dake yammacin nahiyar Afrika ta kawar da annobar cutar a cikin watan Satumban da ya gabata.

An gano matashin yana dauke da cutar Ebola a ranar 19 ga watan Nuwamba a yankin Du-Port Road dake arewacin Monrovia, babban birnin kasar.

Mataimakin ministan kiwon lafiya na kasar, Francis Kateh, ya bayyana cewa, matashin ya rasu ne a ranar Talata a yayin da yake samun jinya a wani asibitin kula da masu cutar Ebola. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China