in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan sandan MDD na taimakawa Mali wajen binciken harin ta'addanci
2015-11-24 11:02:52 cri

Rahotanni na nuna cewa, 'yan sandan MDD suna taimaka wa gwamnatin kasar Mali da fasahohi da dabarun bincike game da mummunan harin ta'addancin da ya faru a ranar Jumma'ar da ta gabata a otel din Radisson Blu.

A ranar 20 ga watan nan ne dai aka kai harin ta'addanci, kuma jami'an tsaro daga bangaren tsaro da ba da kariya da kuma bangaren saurin maida martani da bangaren 'yan sanda na tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD wato MINUSMA sun kasance a harabar tare da ma'aikatan jinya da motocin daukan marasa lafiya da na kashe gobara domin ba da tallafin da ake bukata, in ji wani jami'in ofishin MINUSMAn.

Yan sanda guda 45 na majalisar wato UNPOL da jami'an tsaro 14 na majalissar suna cikin wannan ayari, a cewar Hamdi, wani jami'in majalissar a bayanin da ya fitar. Yana mai jaddada cewa, har yanzu 'yan sandan na UNPOL suna ci gaba da aiwatar da bincike.

MINUSMA ta yi suka mai tsanani ga duk wani aikin da zai kawo cikas ga wanzar da zaman lafiya, kuma a shirye take ta ci gaba da ba da taimakon da ya kamata ga al'umma da gwamnatin kasar Mali a kokarin da ake na dawo da dawwamanmen zaman lafiya a kasar.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China