in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hare haren Bamako da Kidal yunkuri ne na gurgunta zaman lafiya a Mali
2015-03-10 13:27:24 cri

Harin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 5 a Bamako, da harin da aka kai kan sansanin MDD da ke kasar Mali na tawagar MINUSMA da ya halaka wani jami'in wanzar da zaman lafiya na MDD da fararen hula biyu, ayyuka ne na masu gaba da zaman lafiya, in ji ministan sadarwan kasar Mali kuma kakakin gwamnati, Choguel Kokalla Maiga, a yayin wani taron menama labarai.

An sanya hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya a ranar daya ga watan Maris din da ya gabata a birnin Alger na kasar Aljeriya tsakanin gwamnatin Mali da kungiyoyi masu dauke da makamai dake arewacin Mali.

Ministan ya gayyaci sauran kungiyoyi masu dauke da makamai da su sanya hannu kan wannan kundin zaman lafiya, tare da yin alkawarin cewa, gwamnatin Mali za ta yi iyakacin kokarinta domin ganin wannan yarjejeniya ta kasance tushen zaman lafiya a kasar. A ko da yaushe idan ana kan wani muhimmin lokaci na zaman lafiya, akwai abokan gaba ga zaman lafiya dake kokarin kawo cikas da yin zagon kasa domin kawo rauni ga wannan yarjejeniya. Kuma hare haren baya bayan nan da aka kai suna cikin tsarin masu gaba da zaman lafiya. Dalilin haka ne, a cewar mista Kokalla Maiga, ya kamata mu nuna natsuwa, mu rike hanyar da ba za ta karkata gwamnati da al'ummar kasar Mali ba domin tsaya ga neman wata yarjejeniyar zaman lafiya mai dorewa a kasar Mali, ta yadda gamayyar kasa da kasa za ta yi maraba da hakan. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China