in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi allawadai da sabon harin da ya halaka sojan MDD 'dan asilin Senegal a Mali
2014-10-09 14:57:44 cri

Sakatare janar na MDD, Ban Ki-moon tare da kwamitin tsaro sun yi allawadai da wani sabon hari a ranar Talata a kasar Mali da ya halaka wani sojan wanzar da zaman lafiya 'dan kasar Senegal tare da raunana wani guda.

Sakatare janar ya nuna bacin ransa game da harin da ya abku jiya ranar 8 ga wata a kasar Mali, in ji kakakinsa a cikin wata sanarwa.

A yayin wannan hari na biyu, kwanaki biyar bayan wanda aka kaiwa tawagar MINUSMA, wasu mahara da ba'a tantance su ba, sun jefa nakiyoyi shida zuwa sansanin tawagar dake Kidal. Wannan hari ya kai ga cimma yawan sojojin wanzar zaman lafiya 31 da suka mutu, tare da jikkata mutane 91 tun bayan ranar daya ga watan Yulin shekarar 2013. Ban Ki-moon ya sake tunatar da nauyin da ya ratawa ga dukkan bangarorin da su hana a kai hare-hare kan sojojin MDD, tare da jaddada muhimmancin cimma mafitar siyasa da za ta kasance hanya daya tak ga kai ga zaman lafiya da zaman karko a kasar Mali, in ji kakakin Ban Ki-moon.

A cikin wata sanarwa, kwamitin tsaro ma ya yi allawadai da wannan harin tare da bayyana cewa, kai hari kan sojojin wanzar da zaman lafiya babban laifin yaki ne. Ya kuma bukaci gwamnatin kasar Mali da ta gudanar da binciken gaggawa kan wannan harin.

Mambobin kwamitin tsaro sun sake yin kira ga kungiyoyi masu makamai dake arewacin kasar Mali kan niyyar da su dauka ta yin aiki tare da MDD domin rigakafin hare-hare kan sojojin wanzar da zaman lafiya, kamar yadda sanarwar da aka rattabawa hannu a ranar 16 ga watan Satumban shekarar 2014 a birnin Alger ta tanada, in ji kwamitin. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China