in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban sifeton 'yan sandan Najeriya ya lashi takobin murkushe masu tada kayar baya
2015-09-25 10:06:25 cri

Babban sifeton 'yan sandan Najeriya Solomon Arase ya ci alwashin yakar masu tada kayar baya a kasar.

Mista Arase ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua a ranar Alhamis din nan cewar, a yanzu haka kimanin jami'ansa dubu 4 ne ke gudanar da aikin hadin gwiwa da sojojin kasar a ci gaba da farautar masu tada kayar baya a yankin arewa maso gabashin kasar.

Ya ce, an kai mataimakin kwamishinan 'yan sanda a helkwatar 'yan sanda dake Maiduguri domin tafiyar da ayyukan hukumar yadda ya kamata.

Arase ya ce, hukumar 'yan sandan ta baza jami'anta a dukkanin sassan kasar domin su tabbatar da tsaron rayukan al'ummar musulmin kasar a yayin gudanar da bukukuwan babbar sallar a jiya Alhamis.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China