in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya na shawarar dawo da sojojinta daga wasu kasashe domin karfafa tsaro
2015-01-23 10:21:57 cri

Mahukunta a Najeriya na shawarta dawo da wasu daga dakarun sojin kasar dake aikin wanzar da zaman lafiya a wasu kasashe, domin shiga ayyukan karfafa tsaron yankunan arewa maso gabashin kasar.

A cewar shugaban ofishin tattara bayanai a Najeriyar Mike Omeri, hakan na cikin batutuwan da aka tattauna, tsakanin wakilan Najeriyar da sauran masu ruwa da tsaki a ranar Talata, yayin taron tsaro da ya gudana a birnin Yamai na kasar Nijar.

Jami'in dai bai bayyana kasashen da za a janyewa sojojin ba, sai dai ya ce, taron na birnin Yamai, ya biyo bayan rushewar shirin hadin gwiwa na yaki da ayyukan kungiyar Boko Haram, da kasashe makwaftan Najeriyar suka shiga a baya.

Omeri ya ce, yayin taron, an mikawa kwamitin tsaron MDD bukatar neman amincewar kafa wata kakkarfar tawagar hadin gwiwa, wadda za ta iya tunkarar masu tada kayar baya, karkashin inuwar kungiyar AU.

Kaza lika Najeriya ta bukaci kasashe makwaftanta, da su kara kwazo wajen kare kan iyakokinsu domin cimma burin da aka sanya gaba. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China