Rundunar 'yan sanda a Najeriya ta bayyana daukar karin matakan tsaurara tsaro a dukkanin fadin kasar, sakamakon karatowar bukukuwan kirsimeti da na sabuwar shekara.
Kakakin rundunar na kasa Emmanuel Ojukwu ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labaru.
Ojukwu ya ce, 'yan sanda za su fara gudanar da wani shiri na musamman, da zai kunshi yaki da ayyukan ta'addanci, da tattara bayanan sirri, domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al'ummar kasar.
Ya ce, babban sifeton 'yan sandar kasar Suleiman Abba, ya umarci daukacin sassan rundunar da su tabbatar da ba da kariya ga al'umma a wannan lokaci na bukukuwa.
Sanarwar ta kuma yi kira ga masu gudanar da harkokin da ke tara jama'a, da su tabbatar da tantance abokan huldar su, musamman ma a wannan lokaci na bukukuwa.
Daga nan sai sanarwar ta ja hankalin jama'ar kasar da su kai rahoton duk wani abu, ko wani mutum da ba su amince da shi ba ga 'yan sanda, domin daukar matakan da suka wajaba.
A baya bayan nan Najeriya na fuskantar karin hare-haren kunar bakin wake, ciki hadda tashin bama bamai a jiya Litinin, a tashoshin motocin jihohin Gombe da Borno. Bayan ga harin garin Bajogan jihar Gombe, wadanda suka sabbaba rasuwar mutane da dama. (Saminu)