in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
ECOWAS za ta shirya wani taro kan rikicin Burkina Faso
2015-09-22 10:10:28 cri

Kungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS) za ta shirya wani taron gaggawa kan rikicin Burkina Faso a ranar yau Talata a birnin Abuja, hedkwatar Najeriya.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ba da wannan labari a cikin wata sanarwa. Tare da yin allawadai da juyin mulki a Burkina Faso, shugaba Buhari ya yi kira da a maido tsarin mulki nan take na hukumomin rikon kwarya, kuma ya yi kira ga daukacin sojoji da jami'an tsaro na Burkina Faso da su ba da yardarsu ga tsarin mulki na wucin gadi.

A farkon wannan wata, Najeriya ta baiwa hukumar zaben Burkina Faso kyautar motoci 20 domin gudanar da zabuka yadda ya kamata.

Shugaban Senegal Macky Sall da takwaransa na Benin Boni Yayi sun isa Burkina Faso a ranar Jumma'a da ta gabata domin sulhunta rikicin siyasa bayan juyin mulki da sojojin kasar suka yi a ranar 16 ga watan Satumba.

Macky Sall shi ne shugaban kungiyar ECOWAS a yayin da Boni Yayi yake mai shiga tsakani game da rikicin Burkina Faso. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China