Shugaba John Dramani Mahama a ranar Laraban nan ya tashi zuwa kasar Burkina Faso dake makwabtaka da kasar ta Ghana domin taimakawa a maido da shirin gwamnatin wucin gadi yadda ya kamata, kamar yadda wata sanarwa daga fadar shugaban ta bayyana.
Wannan dai ya biyo bayan shawarar da kungiyar ECOWAS ta yi ta tabbatar da sake maida gwamnatin wucin gadi yadda aka tsara a kasar.
Yan gadin fadar shugaban kasar a ranar Alhamis din makon da ya gabata ne dai suka sanar da hambarar da gwamnatin wucin gadin da kwamitin kula da kafa gwamnatin kasar ta kafa a bara tare da taimakon kungiyar ECOWAS.
Da suke tattauna rikicin siyasar a zaman taron musamman a Abuja a ranar Talata, shugabannin kasashe da gwamnatocin kungiyar ECOWAS din sun yi kakkausar suka ga harin da masu gadin fadar shugaban kasar suka kai wa gwamnatin wucin gadin kasar.
Shugabannin kasashe na kungiyar ECOWAS daga nan sun zabi Thomas Boni Yayi na Benin, Faure Gnassingbe na Togo, Muhammadu Yusufu na Jamhuriyar Niger da shugaban Ecowas na wannan karon kuma shugaban kasar Senegal Macky Sall da su kafa wani kwamiti na musamman domin aiwatar da aikin maido da gwamnatin wucin gadin a kasar ta Burkina Faso.(Fatimah)