Hukumomi a Burkina Faso, sun fada a jiya Laraba cewar, zaben shugaban kasar da aka shirya gudanarwa ranar Asabar ta makon nan, an dage shi zuwa ranar 29 ga watan Nuwamban shekarar nan.
Dukkanin jam'iyyun siyasa da ita kanta majalisar ministocin kasar sun yi na'am da sabuwar ranar da aka sanya don gudanar da zaben..
Gabannin dage zaben, da farko jam'iyyun siyasa da kungiyoyin fararen hular kasar sun cimma yarjejeniya cewar, za'a gudanar da manyan zabuka ciki har da na shugaban kasar ne a ranar 11 ga watan Oktoban wannan shekara. (Ahmad Fagam)