Jihar Jigawa dake arewacin Nigeriya ta ce, za ta dauki nauyin dalibanta marasa galihu guda 50 domin zuwa kasar Sin su karanta likitanci.
Gwamnan jihar Muhamadu Badaru ne zai rattaba hannu a kan yarjejeniyar hakan da makarantun horas da likitocin kasar Sin a ziyarar da zai kawo kasar, in ji kwamishinan lafiya Abba Umar.
Kamar yadda kwamishinan ya yi wa manema labarai bayani a ranar Litinin din nan, ya ce, za'a dauki dalibi daya daga cikin mazabu 30 na jihar a zaben da za'a yi daidai wa daida tsakanin maza da mata.
Ya ce, za'a tantance daliban da suka nemi gurbin karatun domin a zabi zakara a cikin su, a cewar shi, wannan zai kara wa bangaren kiwon lafiya a jihar samun kwararru.(Fatimah)