in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Ghana ya kaddamar da cibiyar sarrafa iskar gas da kamfanin Sin ya gina
2015-09-17 11:07:12 cri

A ranar larabar nan ne shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama, ya kaddamar da cibiyar sarrafa iskar gas mallakar kasar wanda kasar Sin ta gudanar da aikin irin sa na farko a kasar wanda ke yankin Atuabo dake da tazarar kilomita 218 zuwa babban birnin kasar.

Aikin wanda ya lakume miliyoyin daloli, wani katafaren kamfanin aikin samar da man fetur da iskar kasar Sin Sinopec ne ya gudanar da aikin.

Cibiyar wanda ke da karfin sarrafa Cubic miliyan 120 na iskar gas ko wace rana daga filin man fetur na Jubilee a kullum kuma zai iya samar da gas ga kogin Volta wanda zai rika samar da makamashi domin ba da hasken wutar lantarki ga kasar.

Shugaba Mahama na kasar ta Ghana ya ce, wanann katafaren aikin zai iya zama tamkar wani sabon sauyi ne, musamman wajen rage nauyin da kananan cibiyoyin samar da lantarkin kasar ke fuskanta.

Shugaba ya yabawa gwamnatin kasar Sin a madadin al'ummar kasar Ghana, sannan ya jinjinawa kamfanin na Sinopec saboda samar musu rance da kammala aikin a kan lokaci gami da samar musu da kwararrun jami'ai.

A nasa jawabin, jakadan kasar Sin a Ghana Sun Baohong, ya ce, kammala aikin zai baiwa kasar ta Ghana damar sarrafa iskar gas dai dai da bukatar kasar, har ma zai bunkasa wasu bangarorin kasar da dama.

Shi ma shugaban rukunin kamfanonin sarrafa iskar gas na kasar Ghana Alfred Ogbamey, ya ce, cibiyar za ta samar da ilmi da kuma kwarewa ga al'ummar kasar ta Ghana.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China