in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manzon MDD ya bukaci bangarorin Libya da su ci gaba da yin shawarwari
2015-07-16 09:52:15 cri

Manzon musamman na MDD da ke kasar Libya Bernardino Leon ya bukaci daukacin bangarorin da ke rikici a Libya, da su ci gaba da shawarwarin da suke yi na ganin an maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.

Jami'in na MDD ya bayyana hakan ne lokacin da yake yiwa kwamitin sulhu na MDD bayani game da yanayin da ake ciki a kasar. Inda ya jaddada kudurin majalisar na hukunta duk wanda aka kama yana kokarin kawo kafar ungula ga shirin.

Mr Leon ya ce, muddin ana bukatar shirin ya samu nasara, to wajibi ne a hada kai tare da goyon bayan gwamnatin hadaka da ake fatan kafawa a nan gaba. Ya kuma yi imanin cewa, idan har aka samar da cikakken tsaro a birnin Tripoli, da ma kasar baki daya, hakika al'amuran gwamnatin za su dawo dai-dai a kasar.

A ranar 11 ga watan Yuli ne wasu bangarorin kasar suka kirkiro shirin sasanta rikicin siyasar kasar a kasar Morocco, matakin da ake ganin zai kawo karshen rikicin kasar, tare da bude kafar kara yin tattaunawa.

Tun a karshen watan Satumban bara ne dai MDD ta sha shirya tattaunawa tsakanin bangarorin da ke fada da juna a kasar, amma duk da yarjejeniyar da suka cimma, har yanzu ana ci gaba da gwabza fada.

Kasar Libya dai ta fada cikin tashin hankali ne tun lokacin da boren siyasar kasar na shekarar 2011 ya yi awon gaba da tsohon shugabar kasar Muammar Gaddafi. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China