Rundunar sojin Najeriya ta gargadi al'ummar kasar, musamman masu gidajen kallon kwallon kafa, da masu sha'awar kwallon da su sanya ido kwarai yayin gudanar gasar cin kofin duniya dake tafe.
Kakakin rundunar sojin manjo janar Chris Olukolade ne ya ja hankalin al'ummar kasar, yayin taron ganawa da 'yan jaridu da ya gudana a Abuja, babban birnin tarayyar kasar.
Olukolade ya ce, ya zama wajibi al'umma su rika lura da mutane ko abubuwan dake kusa da su, yayin gudanar gasar cin kofin ta duniya, domin kaucewa makamancin harin da ya auku a jihar Adamawa a Lahadin da ta gabata. Ya ce, rundunar sojin kasar na matsa kaimi wajen dakile hare-hare kan fararen hula, a daukacin yankin arewa maso gabashin kasar, yankin da a yanzu haka ya fi fama da tashe-tashen hankula.
Har ila yau Olukolade ya bayyanawa 'yan jaridun cewa, a yayin wani simame da dakarun rundunar sojin kasar suka gudanar a jihar Benue dake tsakiyar kasar, sun samu nasarar harbe wasu 'yan ta'adda su biyar, tare da kwace bindigogi da motoci biyu daga gare su. (Saminu)