Wasu kamfanonin kasashen Sin da Najeriya suna kokarin farfado da kamfanin mulmula karafa na Ajaokuta da ke tsakiyar tarayyar Najeriya, inda aka yi kiyasin cewa, za a samar da tan miliyan 2 na karafa cikin shekaru biyu da fara aikin kamfanonin.
Shugaban kamfanin sarrafa manyan na'urori na kamfanin Henan Taihang Quanli, Huang Quanli ne ya bayyana hakan jiya yayin da yake gabatar da kamfanin a wani taro da ya gudana a Abuja.
Ya ce, kamfanin wanda ya kunshi kamfanin sarrafa karafa na Total Steel Ltd Nigeria da kamfanin sarrafa manyan na'urori na Henan Taihang Quanlin, an kafa su ne domin su karbi aikin kamfanin na Ajaokuta da ya dade ba ya aiki.
Ya ce, sun ziyarci kamfanin na Ajaokuta, kuma sun gamsu da yanayin da injunan kamfanin ke ciki, duk da cewa, sun daina aiki na kusan tsawon shekaru 30 saboda yadda aka yi watsi da kamfani sakamakon rashin kammala shi.
Don haka ya ce, cikin 'yan shekaru kalilan Najeriya za ta kasance kasa mai dogaro da kanta, kana mai fitar da dukkan kayayyakin da suka shafi karafa zuwa kasashen da ke makwabtaka da ita, muddin aka ba su damar zuba jari a kamfannin sarrafa karafa na Ajaokutan.
A jawabinsa, shugaban kamfanin sarrafa karafa na Total, Hussaini Abdulraham, ya ce, aikin zai taimaka wajen rage shigo da karafa daga kasashen waje samar da ilimin sana'o'i a kasar ta hanyar hakowa da sarrafa albarkatun kwal, tama da farar kasa da Allah ya horewa kasar ta Najeriya. (Ibrahim)