in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Santos na Angola ya gana da wakilin Sin
2015-11-13 09:19:09 cri

Wakilin kasar Sin mai lura da al'amuran da suka shafi nahiyar Afirka Zhong Jianhua, ya isar da sakon fatan alheri na shugaba Xi Jinping ga gwamnatin Angola, game da cikar kasar shekaru 40 da samun 'yancin kai.

Mr. Zhong wanda ya bayyana wannan sako yayin zantawar sa da shugaban Angola Jose Eduardo dos Santos a jiya Alhamis, ya ce, gwamnatin kasar Sin na martaba alakar dake tsakanin ta da kasar Angola. Har ila yau ya jinjinawa irin ci gaban da kasar ta samu, tun samun 'yancin kai kawo wannan lokaci.

Wakilin na Sin ya kuma bayyana aniyar kasar Sin ta tabbatar da an aiwatar da manufofin bunkasuwa tsakanin kasashen biyu, da ma yarjejeniyoyin da shuwagabannin kasashen suka cimma, yayin ziyarar da shugaba Santos ya gudanar a kasar Sin cikin watan Yunin da ya gabata.

Da yake maida jawabi, shugaba Santos ya godewa irin kwazo da Sin ke nunawa wajen tabbatar da ci gaban Angola, yana mai cewa, kasar sa ta bude wani sabon babi na bunkasa, za kuma ta zurfafa hadin gwiwa da Sin a dukkanin fannoni, musamman ma kan al'amuran da suka jibanci zuba jari da hada-hadar kudade.

Bugu da kari shugaban na Angola ya ce, kasar sa na da burin bunkasa hadin gwiwa da Sin a fannin fadada jarin Sin a kasar ta Angola.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China