in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi Allah wadai da afkawa jami'anta a CAR
2015-10-20 09:33:09 cri

Mai magana da yawun MDD Stephane Dujarric ya ce, majalisar ta yi Allah wadai da kai hari kan tawagar jami'an dake aikin wanzar da zaman lafiya wato MINUSCA a jamhuriyar tsakiyar Afrika CAR, lamarin da ya sake ta'azzara rikicin da ake fama da shi a kasar.

Rahotanni sun ce, an bude wuta kan 'yan sandan MINUSCA su 7, sannan an tsare su ba bisa ka'ida ba, kuma mayakan anti-Balaka ne suka aikata da yammacin ranar Lahadi kusa da Boali a yankin Ombella Mpoko. Sai dai daga bisani an saki 'yan sandan na MINUSCA a daren Lahadin.

Dujarric ya ce, a ranar Lahadin, mayaka 3 sun kai hari ga wani sansanin MINUSCA a Damara dake yankin Ombella Mpoko, jami'an tsaron MINUSCA sun yi musayar wuta da su, lamarin da ya haddasa mutuwar guda daga cikin mayakan yayin da biyu suka tsere.

MDD ta yi kakkausar suka dangane da afkawa jami'anta, sannan ta bukaci da'a gaggauta bincike don gano wadanda ke da hannu a harin don hukunta su.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China