in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude baje kolin hoton nuna zumunci tsakanin Kenya da Sin a Nairobi
2015-09-02 10:38:49 cri

An bude bikin baje koli na hoto ne dake nuna zumunci tsakanin kasashen Kenya da Sin a birnin Nairobi a ranar Talatan nan domin murnar cika shekaru 2 da aka rattaba hannu kan wata yarjejeniyar hadin gwiwwa tsakanin kasashen biyu.

Yarjejeniyar hadin gwiwwar da shugaban Kenya Uhuru Kenyatta ya rabbata wa hannu a lokacin ziyararsa a kasar Sin a watan Agustan shekara ta 2013, yana da zummar inganta fahimtar juna da moriyar juna daga dukkan bangarori.

Bikin baje hotonan zai dauki wata daya ana yi, inda aka baje hotuna fiye da 50 wanda ke nuna nisan da aka yi wajen zumunci da juna a bangaren siyasa, tattalin arziki da al'adu.

A cewar jakadan kasar Sin a Kenya Mr Liu Xianfa, Sin a shirye take ta yi aiki kafada da kafada da Kenya a bangaren aikin gona na zamani, samar da ababen more rayuwa, kere kere, kare muhalli, al'adu da yawon shakatawa da kuma tsaro.

A nashi bangaren, ministan ma'aikatar wasanni da al'adun Kenya Hassan Wario ya ce, baje kolin hotunan zai kara inganta musanya tsakanin al'ummomin biyu. Yana mai bayanin cewa, kasar Sin ce za ta dauki nauyin gina cibiyar yada al'adun kasar Sin a birnin Nairobi.

A cewar shi, za a kammala cibiyar nan da shekaru biyu, hakan zai taimaka wajen yada al'adun kasar Sin a Kenya, tare kuma da inganta hadin gwiwwar al'adu tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China