Jam'iyyar ANC mai mulki a kasar Afirka ta Kudu ta zartas da wata dokar dake cike da takadama kan bunkasa da kare zuba jari ta wuce da karfi a ranar Talata a gaba kwamitin 'yan majalisa na kasuwanci da masana'antu, duk da babbar adawar daga bangaren masu hada hada da kuma jam'iyyu masu adawa.
Dokar dai za a gabatar da ita gaban majalisar dokoki domin samun shiga.
Lamarin ya zo daidai da lokacin da aka ba da kashedi dake nuna yiyuwar ficewar masu zuba jari 'yan kasashen waje dake kasar ta Afrika ta Kudu bayan amincewa da wannan doka. (Maman Ada)