in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Magatakardar MDD ya yi tir da harin roka kan Isra'ila
2014-03-13 10:52:53 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon ya yi tir a ranar Laraban nan game da harin roka da aka kai wa kudancin Isra'ila yana mai kira ga dukkan bangarorin da hakan ya shafa da su kai zuciya nesa domin kaucewa tsananta halin da yanzu haka ake ciki.

A cikin wata sanarwa da kakakinsa ya fitar, ya ce, magatakardar majalissar ya yi suka da kakkausar murya kan jerin rokoki da aka harba wa Isra'ila daga zirin Gaza wanda wata kungiya mai suna Jihadin musulunci ta dauki alhakin jefawa.

'Yan ta'addan daga zirin Gaza sun harba jerin rokoki fiye da 30 a ranar Laraban nan, a cewar sojin kasar Isra'ila, sai dai babu wanda ya ji rauni ya zuwa wannan lokacin.

Kungiyar Jihadin musuluncin dake Palasdinu daya daga cikin kungiyoyin 'yan ta'adda dake yankin ta dauki alhakin jefa rokokin kamar yadda kafar yada labarai na Palasdinun ta sanar.

Harin na ranar Laraban nan shi ne ya fi tsanani a wurare biyu tun karshen harin kare kai na luguden wuta da Isra'ila ta aiwatar na tsawon kwanaki takwas a zirin Gaza a watan Nuwambar shekara ta 2012.

A martanin da ta fitar, Isra'ila ta ce, ita ma ta mai da wannan sako a sansanoni biyu da 'yan ta'addan suka yi amfani da su wajen mata aiken dake arewaci da kudancin Gaza a yammacin ranar Laraban. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China