in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya nuna damuwa kan shirin Isra'ila na gine-gine a yammacin kogin Jordan
2014-06-06 10:22:58 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon ya bayyana matukar damuwar sa, game da shirye-shiryen da mahukuntan kasar Isra'ila ke yi, na ci gaba da ginin matsugunnan Yahudawa a yankunan yamma da gabar kogin Jodan. Mr. Ban ya kuma yi kira ga mahukuntan kasar ta Isra'ila, da su amsa bukatar da kasashen duniya suka yi, game da dakatar da gine-gine a wannan yanki.

Wannan kira na babban magatakardar MDDr dai na zuwa ne, biyowa bayan wasu rahotanni da ke nuna cewa, Isra'ilan ta fitar da takardun tantance kamfanonin da za a baiwa aikin ginin sabbin gidajen da yawansu ya kai 1,400 a wannan yanki, ciki hadda wasu sassa na birnin Jerusalem.

Wata sanarwa da kakakin Mr. Ban ya fitar ta nanata matsayar MDD game da haramcin gine-gine a wannan yanki na yamma da gabar kogin Jordan. Kaza lika sanarwar ta jaddada kiran da Mr. Ban ya yi wa bangarorin Isra'ila da Falasdinu ran 1 ga watan Mayun da ya shude, game da kauracewa daukar duk wani mataki, da ka iya yiwa shirin wanzar da zaman lafiya tsakanin sassan biyu kafar ungulu. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China