in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kai hari a wani ginin gwamnatin Somaliya
2015-04-15 10:47:38 cri

Aka kashe sojoji 6 da fararen hula 15 a ranar Talata a Mogadishu, babban birnin Somaliya, a harin kungiyar masu kaifin kishin islama ta A-Shabaab ta kai a wani ginin gwamnatin kasar dake kunshe da ofisoshin ministoci biyu.

Kakakin ma'aikatar tsaron Mohamed Yusuf ya tabbatar da cewa, sojojin sun mutu a yayin gumurzu tare da maharan, wanda da farko suka kutsa motarsu cikin ginin mai dauke da boma bomai. Ginin da aka kai wa hari na kunshe da cibiyar ma'aikatar ilimi ta kasa da ma'aikatar man fetur da ma'adinai.

Mun yi asarar sojojin Somaliya 5 da soji guda na tawagar wanzar da zaman lafiya ta kungiyar tarayyar Afrika (AU) dake Somaliya. An kashe dukkan maharan, in ji mista Yusuf. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China