in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MONUSCO ta yi kiran DRC da ta karfafa dangantaka da kasashen shiyyar
2015-09-14 10:23:50 cri

Shugaban tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake DRC-Congo (MONUSCO), Martin Kobler, ya shawarta batun karfafa dangantaka tsakanin gwamnatin DRC-Congo da kasashen shiyyar ta fannin sada zumunci da kuma ta fuskar tsarin kungiyoyin shiyyar, kamar taron kasa da kasa na yankin babban tafki, gamayyar ci gaban kasashen kungiyar SADC, da kuma kungiyar ci gaban tattalin arzikin kasashen tsakiyar Afrika ta CEEAC.

Domin samun ci gaba mai dorewa, ya zama wajibi a tabbatar da dangantaka ta bangaren tsaro a shiyyar babban tafki, in ji mista Kobler a cikin wata sanarwar da aka fitar a ranar Asabar, albarkacin ranar dangantakar kudu da kudu ta MDD, da aka yi bikinta a ranar 12 ga watan Satumba.

Ina nuna yabo ga gwamnatin Congo kan kokarinta na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ta hanyar karfafa dangantakar kudu da kudu, in ji mista Kobler.

Kasashe masu tasowa suna bukatar ci gaba da aiwatar da dangantakar kudu da kudu domin samun tattalin arziki na gaskiya, da kuma kyautata halin rayuwar jama'a, a cewar wannan jami'i.

Tare da sanya hannu kan yarjejeniyar tsari ta Addis Abeba, kasashen shiyyar sun dauki niyyar hada karfi da karfe domin karfafa zaman lafiya da shimfida dangantakar tattalin arziki mai karfi.

A cewar manyan jami'an MDD, duk da wasu matsalolin da ake fuskanta, kasashe masu tasowa sun kasance a sahun gaba wajen taka muhimmiyar rawa ta fuskar ci gaban tattalin arziki da na jama'a a duniya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China