Wasu kauyuka biyu masu tazarar kilomita kusan dari daga Aru-Centre, a gundumar Ituri, dake gabashin kasar DRC-Congo, sun samu kwararar 'yan kasar Sudan ta Kudu.
Wata tawagar 'yan majalisa na Ituri sun tabbatar da wannan lamari, bayan wata ziyarar gani da ido da suka kai a ranar Jumma'ar da ta gabata a wannan yanki na kasar.
Al'umomin wani kauyen Sudan ta Kudu dake iyaka da kasar DRC-Congo na shigowa sannu hankali cikin kasarmu, in ji shugaban 'yan majalisun Ituri, mista Joas Mbitso Genza.
A cewar wadannan 'yan majalisa, suna kokarin sanar da hukumomin Kinshasa kan halin da ake ciki, domin su dauki wannan matsala da muhimmanci domin kaucewa ganin abubuwan tashin hankali na iyakar Vura tsakanin DRC-Congo da Uganda ba za su sake faruwa ba tare da Sudan ta Kudu.
Muna kallo wannan matsala a matsayin mamaye fadin kasar Congo da Sudan ta Kudu ke yi, in ji Joas Mbitso Genzo, dake kuma nuna damuwa kan wannan matsala da ka iya dagula dangakantakar makwabataka tsakanin kasashen biyu.
A cikin watan Yunin da ya gabata, wani gungun 'yan sandan Uganda dauke da makamai, tare da rakiyar kwamishinan 'yankin iyakar Nebbi na Uganda tare da DRC-Congo ya yi kutse cikin kasar Congo. (Maman Ada)