in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNSMIL ta sake gusa zaman taron sassanta 'yan kasar Libiya
2015-01-05 10:14:52 cri

Tawagar MDD kan kasar Libiya (UNSMIL) ta dauki niyya a ranar Lahadi na gusa zaman taron shawarwari tsakanin jam'iyyun siyasa na kasar Libiya, da aka tsai da shiryawa a ranar biyar ga watan Janairu, in ji wani dan majlisar kasar Libiya. Mambobin majalisar dokoki sun tuntubi jami'an tawagar UNSMIL domin sanin gyare gyaren karshe da suka shafi zaman taron shawarwarin da ya kamata a fara a wannan ranar Litinin. Amma tawagar MDD dake kasar Libiya ta bayyana cewa, ta gusa wannan lokaci, in ji wani dan majalisa da ya bukaci a sakaya sunansa a yayin da yake hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

Ba a ba da wata hujja ko dalilin gusa wannan zaman taro ba, in ji wannan dan majalisa. A nasa bangare, mista Omar Hemeidan, kakakin babban zauran kasa (CNG), wato majalisar dake barin gado, ya tabbatar da gusa wannan taro, tare da nuna cewa, UNISMIL ta sanar CNG cewa, ba a tsai da wani lokaci ba, a yayin da yawancin ma'aikatan tagawar suke gudanar da hutun sabuwar shekara a kasashen waje. Wannan shi ne karo na uku da ake gusa wannan zaman taro a karkashin tawagar MDD. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China