Tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake kasar Libya UNSMIL ta bayyana cewar, a mako mai zuwa ne kungiyoyi masu fada da juna za su koma bisa teburin tattaunawa domin kaiwa ga samar da zaman lafiya a kasar, wacce ta fada cikin yaki tun bayan rasuwar tsohon shugaban kasar Muammar Gaddafi.
Za'a gudanar da tattaunawar zaman lafiyar a karkashin shiga tsakani na MDD, wacce ita ce ta yi sular samar da tattaunawar sulhu tsakanin sassan biyu.
Wata sanarwa tawagar MDD ta ce, da za ran an kammala shirye-shiryen taron da samar da matakan tsaro, za'a sanar da dandalin da za'a gudanar da taron da kuma takamaiman lokacin taron.
Sanarwar ta ce, a mako mai zuwa za kuma a gudanar da wani makamancin taron tattaunawa a Geneva dake Switzerland a inda daukacin jam'iyyun siyasa da masu kare hakkin bil'adama na kasar Libya za su hallara.
Sanarwar ta ce, za kuma a gudanar da wani taron wanda zai kunshi kwamandojin kungiyoyin dake fada da juna domin shirya su tunkarar taron samar da zaman lafiyar da za'a yi.
Taron wanzar da zaman lumana a Libya yana da muradin kaiwa ga yarjejeniyar yadda za'a tafiyar da canjin siyasa a Libya, tare da kafa gwamnatin hadin gwiwa da kuma kawo karshen fadace-fadacen da ake fama da su a sassa dabam-dabam na kasar. (Suwaiba)