in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shiga matakin shimfida karafunan layin dogo na Nairobi-Mombasa a kasar Kenya
2015-11-02 10:37:54 cri
Sabon layin dogo a kasar Kenya dake tashi daga Nairobi zuwa Mombasa ya shiga matakin shimfida karafunan layin dogon a wannan mako, kuma za a kammala ayyukan gina hanyar a cikin watan Junin shekarar 2017.

Sabon layin jirgin kasa, mai tsawon kilomita 254, zai hada babban birnin Kenya da muhimmiyar tashar ruwansa ta Mombasa. Kudin wannan aiki an kiyasta su zuwa dalar Amurka biliyan 3,8 da kuna kashi 90 cikin 100 suka fito daga kasar Sin, da kuma kamfanin CRBC na kasar Sin yake ginawa.

Robert Ye, wani manajan kamfanin CRBC, ya bayyana wa 'yan jarida a birnin Mombasa cewa aikin shimfida karafunan layin dogon zai kammala a shekarar 2016. An gudanar da bikin kaddamar da wannan aiki a ranar Jumma'a, lamarin da ya taimaka wajen ganin aikin shimfida wadannan karafuna.

Xu Xin, mataimakin injiniya na sashe na shida na aikin shimfida layin dogon, ya tabbatar da cewa, kimiyyar shimfida layukan dogo na samun ci gaba cikin sauri kuma akwai nau'rori dake maye gurbin yawancin aikin dan adam domin gudanar da ayyuka cikin sauri kuma yadda ya kamata.

Ma'aikata da dama na wurin sun samu horo domin gudanar da ayyuka, kuma yawan ma'aikatan Kenya dake aikin shimfida karafunan layin dogo ya rubanya shi har sau biyu. Hakazalika, ya zuwa yanzu kamfanin kasar Sin ya dauki ma'aikatan Kenya fiye da dubu 25 domin wannan aiki, in ji mista Xu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China