in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta jagoranci dandalin baje kolin CAC a Kenya
2015-09-16 10:03:09 cri
Jakadan kasar Sin a Kenya Liu Xianfa, ya ce kasarsa na fatan taimakawa Kenya da dabarun bunkasa aikin gona, a wani mataki na cimma nasarar fadada kudurin kasar na samar da isasshen abinci.

Mr. Liu wanda ya bayyana hakan a yayin bikin bude taron baje kolin harkokin samar da sinadaran kare tsirrai, da harkokin cinikayyar amfanin gona ko CAC a takaice, wanda aka bude ranar Talata a gundumar Nakuru dake kasar ta Kenya, ya kara da cewa Sin na da kwarewa a fannin noma na zamani, da fannin samar da sinadaran kare amfanin gona, don haka take fatan gudanar da hadin gwiwa da Kenya a wannan fanni.

Ya ce ya dace mahalarta dandalin na wannan karo daga kasashen biyu, su yi amfani da wannan dama wajen karfafa hadin kansu, domin cin gajiyar sabbin fasahohin noma, da kuma kirkire-kirkiren dake taimakawa wannan muhimmiyar sana'a. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China