Hukumar zaben a Tanzaniya ta fada a ranar Litinin din nan cewar, ta fara tsaurara tsaro a helkwatocin hukumar don ba da kariya ga kayayyakin aikin zabe, a yayin da kasar ke sa ran gudanar da manyan zabukan a ranar 25 ga watan Oktoban wannan shekara.
Daraktan hukumar zaben kasar Kailima Ramadhani ya ce, tuni babbar helkwatar hukumar zaben kasar dake Dares Salaam ta kakkafa na'urorin daukar hotuna dan a bincike domin tabbatar da tsaro.
Ramadhani ya kara da cewar, ana ci gaba da kokarin inganta tsaron, an samar da sabbin makullai irin na zamani wadanda za'a maye gurbin tsoffin da ake da su.
Ya ce, suna daukar wadannan matakai ne domin kaucewa satar muhimman kayayyakin aikin zabe da kuma takardun da abin ya shafa.
Sama da mutane miliyan 23 daga cikin adadin al'ummar Tanzaniya miliyan 46 ne za su kada kuri'unsu a zaben shugaban kasar da na majalisun dokoki.
Dan takarar jam'iyyar dake mulkin kasar Chama Cha Mapinduzi, John Magufuli, zai fuskanci abokin hamayyarsa, Edward Lowassa na babbar jam'iyyar adawa ta Chama Cha Demokrasia na Maendeleo wato CHADEMA a takaice. (Ahmad Fagam)