in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta tabbatar da cewa, an ci zarafin mutane 13 a CAR
2015-08-21 09:50:19 cri

Wata babbar jami'ar MDD da ke Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya(CAR) ta bayyana cewa, sun samu rahotannin zargin cin zarafin jama'a guda 13 da aka aikata a kasar a shekara da ta gabata, ciki har da wadda aka yiwa wata karamar yarinya 'yar shekara 11.

Mataimakiyar babban sakataren MDD ta musamman a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, kana mai rikon mukamamin shugabar tawagar wanzar da zaman lafiya a kasar (MINUSCA) Diane Corner ce ta bayyana hakan yayin da take zantawa da manema labarai ta na'urar bidiyo a hedkwatar majalisar dake birnin New York.

Jami'ar ta bayyana kudurin tawagar MINUSCA na gudanar da cikakken bincike don zakulo wadanda ake zargi da aikata wannan danyen aiki, tare da gurfanar da su a gaban kuliya, idan har kasashen dake cikin tawagar suka gaza gudanar da bincike cikin kwanaki 10 da aka ba su.

An nada Corner bisa wannan mukami ne, bayan da Babacar Gaye ya aje mukaminsa bisa yawaitar rahotannin da ake samu na cin zarafin mata da ake zargin dakarun MINUSCA da aikatawa.

Miliyoyin 'yan kasar Afirka ta Tsakiya ne suka bar kasar, tun lokacin da fada ya barke a kasar a shekarar 2013, kana sama da mutane 6,000 suka rasa rayukansu. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China