in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar sojin Nigeriya ta yi gargadin karshe ga Boko Haram
2015-10-21 09:55:02 cri

Rundunar sojin Nigeriya a ranar Talatan nan ta yi gargadin karshe ga 'yan kungiyar Boko Haram dake kai hare hare a yankin arewa maso gabashin kasar.

Kamar yadda kakakin rundunar a yankin Kanar Sani Usman ya bayyana a cikin wata sanarwa da aka ba kamfanin Xinhua, ya ce, suna sanar da kungiyar cewa, rundunar ta san duk maboyarsu, sansanoninsu da duk inda suke ganin suna zaune. Don haka, in ji shi, kamata ya yi su yi koyi da sauran 'yan kungiyar da suka mika wuya.

Sanarwa ta yi bayanin cewa, rashin mika wuya yana da mummanar sakamako ga 'yan kungiyar saboda rundunar sojin ta killace su.

Haka kuma kakakin rundunar ya yi kira ga al'ummomin kasashen duniya baki daya da su yi kokarin shawo kan mayakan Boko Haram da masu taimakawa kungiyar da su daina wannan danyen aiki.

Shugaban Nigeriya Muhammadu Buhari ya ba rundunar sojin umurnin ganin sun murkushe kungiyar baki daya nan da watan Disambar wannan shekara.

Kungiyar Boko Haram dai tana yaki da gwamnatin Nigeriya ne a kokarinta na son kafa daular musulunci, a cewarta, abin da ya sa take ta kai hare hare a jihohin arewa maso gabashin kasar, da ma babban birnin tarayyar Abuja a cikin 'yan shekarun nan.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China