in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An hallaka 'yan bindiga 2 da soja 1 a harin da ake zargin Boko Haram suka kai
2015-10-15 10:50:46 cri

Rahotanni daga Nigeriya sun tabbatar da cewa, an hallaka wassu 'yan bindiga 2 da wani jami'in soja 1 a wani harin da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne suka kaddamar a garin Okene na jihar Kogi.

Kamar yadda wata sanarwa da bangaren sojin kasar ya fitar, an ce rundunar na bincike a kusa da wani masallaci lokacin da aka kai musu harin da misalin karfe 5.30 na asuba, kuma nan take sojojin suka mai da martini, abin da ya yi sanadiyar mutuwar maharan guda 2 da kuma soja daya daga bangarensu, kuma wani soji daban ya ji rauni..

Haka kuma sanarwar ta tabbatar da cewar, wadansu mutane 7 sun mutu, ciki har da 'yan kunar bakin waken uku a wassu jerin hare hare guda 3 da aka kai a garin Maiduguri a yammacin ranar Talata.

Wata sanarwa ta daban kuma daga rundunar sojin ta ce, sun hallaka 'yan kungiyar ta Boko Haram guda 10 a wani samame da suka kai kusa da kauyen Ngollom a makon jiya.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China