in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Zambiya na fatan kara samun zuba jarin Sin a kasarsa
2015-03-26 10:35:32 cri

Shugaban kasar Zambiya, Edgar Lungu ya bayyana a ranar Labara cewa, gwamnatinsa na fatan ganin karuwar zuba jarin kasar Sin a cikin kasarsa bisa wani salon huldar dangantaka tsakanin kamfanonin gwamnati da masu zaman kansu.

Duniya yanzu ta dunkule wuri guda kuma muna kokarin ganin abin da za mu iyar samu daga cikin huldar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, kuma bisa wannan tsarin ne muke neman har kullum wani sakamako na moriyar juna da samun alfanu tare, in ji shugaba Lungu a cikin wata hira tare da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, kafin wata ziyarar aiki da zai kawo a nan kasar Sin a wannan mako. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China