in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Zambiya ya gana da mataimakin shugaban Sin
2014-06-20 10:24:58 cri

Shugaban kasar Zambiya, Micheal Sata ya gana a ranar Alhamis a birnin Lusaka da mataimakin shugaban kasar Sin, Li Yuanchao wanda ke ziyarar aiki a kasar Zambiya. Shugaba Sata, ya bayyana albarkacin wannan ziyarar cewa, ana maraba da zuba jarin kamfanonin kasar Sin a kasar Zambiya. Kuma ya bayyana fatan ganin an karfafa dangantakar cimma moriyar juna dake tsakanin kasashen biyu.

A nasa bangare, mista Li ya tunatar da cewa, kasashen Sin da Zambiya na bikin cikon shekaru 50 da kulla huldar dangantaka tsakaninsu, shi kuma ya jaddada cewa, a tsawon shekaru hamsin da suka gabata, kasashen biyu sun samu babbar moriya bisa tushen dadadar abokantakarsu da ta jurewa kalubalen sauye-sauye a cikin dangantakar kasa da kasa, da kuma yanayin harkokin cikin gida na kasashensu. Kasar Sin na daukar har kullum Zambiya a matsayin 'yar uwa, da kuma abokiyar hulda, kullum a shirye take wajen aiki tare da Zambiya domin bunkasa dangantakar kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi. (Maman Ada)

 

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China