in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin Sin zai zuba jari a bangaren hako ma'adinai a Zambia
2014-07-23 09:57:34 cri

Wani jami'in kamfanin hako ma'adinai na kasar Sin Jinchuan group ya bayyana shirin kamfanin na zuba jarin da ya kai dala miliyan 26.6 a aikin hako ma'adinai a kasar Zambia.

Babban manajan kamfanin Jack Sikamo wanda ya bayyana hakan ya kuma yi kira ga masu sha'awar zuba jari a bangaren hako ma'adinai wadanda ke da lasisi, da su zo su hada gwiwa da kamfanin.

Jami'in ya kuma bayyana cewa, daga shekarar 2010 zuwa 2013, kamfanin ya kashe kimanin dala miliyan 12.7 a aikin hako ma'adinai.

Yanzu haka kamfanin na Jinchuan na kasar Sin, shi ke da kashi 85 cikin 100 na jarin kamfanin Chibuluma, kuma ya bayyana shirinsa na yin hadin gwiwa da kamfanonin cikin gida na kasar don gudanar da aikin hako ma'adinai a kasar ta Zambia.

Bayanai na nuna cewa, kamfanin ya samar da tan 18,000 na tagulla a shekarar da ta gabata, sannan ya zuba jari sosai wajen inganta ayyukansa, tare da fatan kara adadin abin da yake samarwa ya zuwa tan 19,000. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China