in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi zaben shugaban kasar Cote d'Ivoire cikin lumana
2015-10-26 10:03:42 cri

Ayyukan zaben shugaban kasa zagayen farko a kasar Cote d'Ivoire sun gudana a ranar Lahadi cikin kwanciyar hankali, sai dai kuma ba tare da yawan kwararar mutane a rumfunan zabe ba, a cewar wani 'dan jaridar Xinhua a birnin Abidjan.

A cikin yawancin rumfunan zabe, ayyukan zaben sun fara cikin jinkiri na kusan awa daya, dalilin rashin kawo kayayyakin zabe cikin lokaci, har ma da jinkirin kawowa, da rashin kwarewa kan na'urar tantance masu zabe. Wadannan matsalolin sun janyo dogayen layuka a bakin rumfunan zabe. Amma duk da haka, zaben ya gudana a wannan rana cikin lumana, ba tare da wata matsala ba.

Kimanin mutane miliyan 6,3 ake sanya ran sun kada kuri'unsu a cikin mazabu kimanin 19 841 a dukkan fadin kasar da kuma ketare.

Haka zalika, zaben shugaban kasar ya gudana a gaban masu sanya ido na kungiyar tarayyar Afrika (AU), da kungiyar ECOWAS, da kungiyar tafkin Mano da kungiyoyin fararen hula na kasar Cote d'Ivoire. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China